Hukumar Kwastam Ta Kwace Tramadol Da Kudin Su Yakai N1.8Bn Cikin Watanni Uku A Filin Jirgin Saman Legas

0 71

Hukumar Kwastam reshen filin jirgin saman Murtala Muhammed ta kwace fakitin tramadol 23 da kudinsu da ya kai Naira biliyan 1 da miliyan 800 tsakanin watan Janairu zuwa Maris na wannan shekara.

Kwanturolan hukumar kwastam, Mohammed Yusuf, a wani taron manema labarai jiya a Legas, ya ce an shigo da kwayoyin ne daga kasashen Indiya da Pakistan.

Mohammed Yusuf ya lissafa kayayyakin da aka kama da suka hada da fakiti 22 na tramadol mai nauyin miligram 225 da kuma fakiti 12 na tramadol mai nauyin milligram 120.

A cewar Mohammed Yusuf, an gudanar da wadannan kame-kamen ne bisa ayyukan sirri da aka gudanar a filin jirgin.

Ya kara da cewa, an shirya mika kwayoyin tramadol da ke hannunsu ga kwamandan hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA reshen filin jirgin saman Murtala Muhammed.

Leave a Reply

%d bloggers like this: