An Gano Gawarwakin Mutane 6 Da Suka Bace Bayab Wani Kwale-kwalen Da Suke Ciki Ya Kife

0 71

Tawagar masu aikin ceto a kasar Malawi sun sake gano wasu gawarwakin mutane shida da suka bace bayan wani kwale-kwalen da suke ciki ya kife a kogin Shire da ke yankin Nsanje dake kudancin kasar a ranar Litinin.

Mai magana da yawun ‘yan sanda a yankin Nsanje, Agnes Zalakoma, ta ce an tsinto gawarwakin ne a jiya daga wurare daban-daban a bakin kogin.

Agnes Zalakoma ta ce har yanzu ana ci gaba da aikin ceton, bayan afkuwar hatsarin, an ceto mutane 14, yayin da wasu kimanin 20 suka bace.

Tunda farko an gano gawar wani jariri, wanda yana cikin fasinjojin. Kwale-kwalen ya cika makil da mutanen kauye su 37 wadanda ke tsallaka kogin da nufin zuwa yin aiki a gonakinsu a bangaren kasar Mozambique.

Leave a Reply

%d bloggers like this: