Rasha Ta Kai Hari Ta Sama A Birnin Kyiv Na Ukraine A Karo Na Tara A Wannan Watan

0 152

Rasha ta kai hari ta sama a birnin Kyiv na Ukraine a karo na tara a wannan watan.

Jami’an gwamnati sun ce mutum guda ya mutu, wasu biyu kuma sun jikkata a wani hari na makami mai linzami da aka kai kan Odesa, wani birnin tashar ruwa a kudu maso yammacin kasar.

An kuma ji karar tashin bama-bamai a yankunan tsakiyar kasar.

Hukumar soji ta Kyiv ta ce bayanan farko sun nuna cewa an lalata dukkan makamai masu linzami da ake harbowa.

Wannan dai shi ne karo na tara da Rasha ke kai hare-hare ta sama a birnin cikin wannan watan.

Da yake jawabi kafin a ba da cikakken bayani, magajin garin Kyiv Vitali Klitschko ya ce gobara ta tashi a wani garejin da ke birnin amma ya kara da cewa babu wanda ya jikkata.

Shugaban hukumar birnin Kyiv ya ce mayakan Rasha sun kawo wani mummunan hari da makami mai linzami.

Leave a Reply

%d bloggers like this: