Najeriya Ta Shirya Samar Da Gangar Danyen Mai 300,000 Ga Matatar Dangote Domin Fara Aiki

0 85

Hukumar da ke kula da albarkatun man fetur ta Najeriya ta ce ta shirya samar da gangar danyen mai 300,000 ga matatar Dangote domin fara gudanar da ayyukanta.
Shugaban rukunin kamfanin na NNPC, Mallam Mele Kyari ne ya bayyana hakan a yau, yayin da yake gabatar da jawabinsa a wajen bikin baje kolin samar da man fetur da iskar gas da aka gudanar a Bayelsa.
Matatar Dangote, wanda aka bayyana cewa yana da karfin da zai iya tantance man da ake samarwa a kasar nan.
Kamar yadda shafin yanar gizon kamfanin ya bayyana, zai fara aikinsa a ranar Litinin, 22 ga Mayu, 2023.
Ya kuma kara da cewa dole ne Najeriya ta mai da hankali kan samar da iskar gas, ya kara da cewa dole ne kasar ta fara fadada iskar gas.

Leave a Reply

%d bloggers like this: