Gwamnatin Jihar Kano Ta Amince Da Kashe N1.4Bn Ga Daliban Da Zasu Rubuta Jarrabawar Kammala Sakandire Ta Bana

0 80

Gwamnatin jihar Kano ta amince da kashe kudi Naira biliyan 1 da miliyan 403 ga daliban da zasu rubuta jarrabawar kammala sakandire ta bana.
Majalisar zartaswar jihar ta amince da sakin N1,403,936,600 don daukar nauyin dalibai 60,871 da suka cancanta a makarantun sakandire domin rubuta jarrabawar NECO, NABTEB, NBAIS da SSCE.
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Muhammad Garba ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai yayin taron majalisar da aka gudanar a zauren majalisar da ke Kano.
Rukunin daliban da suka ci gajiyar shirin sun hada da wadanda suka samu maki shida da sama da haka, ciki har da Ingilishi da lissafi a makarantun sakandare na yau da kullun a jarrabawar cancanta da manyan daliban makarantun Islamiyya da Tahfeez.

Leave a Reply

%d bloggers like this: