Gwamnatin Jigawa Ta Kaddamar Da Makarantun Tafi Da Gidanka Don Samar Da Ilimi Ga Yara 23,000 Da Basa Zuwa Makaranta

0 102

Gwamnatin jihar Jigawa ta kafa tare da kaddamar da makarantun tafi da gidanka don samar da ilimin farko ga yara 23,000 na makiyaya da aka gano ba sa zuwa makaranta a jihar.
Da take jawabi yayin kaddamar da sabuwar sabuwar fasahar a garin Kiyawa da ke karamar hukumar Kiyawa, babbar sakatariyar hukumar kula da ilimin makiyaya ta jihar, Hajiya Ramatu Muhammad ta ce wani bincike da aka gudanar kwanan nan ya nuna cewa kimanin yaran Fulani makiyaya kusan 25,000 ne suka kasa shiga makarantar.
Kananan hukumomin da suka amfana da wannan aiki sun hada da Guri, Gwaram, Kiyawa, Miga, da Suletankarkar dake jihar da nufin magance matsalar.
Sakataren zartaswar ta yi kira ga makiyayan da su ba gwamnati goyon baya tare da ba gwamnati hadin kai ta hanyar tura ‘ya’yansu makaranta tare da kai rahoton zuwan su ga hukumomin da abun ya shafa

Leave a Reply

%d bloggers like this: