Hukumar lafiya matakin farko ta kasa tace ta fara shirye-shiryen rigakafin cutar corona na bai daya a asibitocin kasar nan ciki har asibitoci masu zaman kansu.

Faisal Shuaib, shine babban daraktan hukumar kuma shine ya bayyana haka a jiya Alhamis, yayin wata zantawa da manema labarai a babban birnin tarayya Abuja.

Wannan dai na nufin asibitoci masu zaman kansu zasu fara aikin rigakafin na corona bisa ka’idojin hukumar.

Ya kuma yi gargadi, dangane da samar da takardar shaidar rigakafin bogi, ya kara da cewa gomnatin tarayya tana aiki da jami’i masu sanya idanu daban-daban.

domin buga misali ga duk wanda yayi yunkurin bayarwa ko sayar da katunan, wanda ya bayyana a matsayin abin kunya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: