Hukumar NAFDAC Ta Rufe Shaguna Biyu a Abuja

0 72

Hukumar kula da ingancin Abinci da Magunguna ta kasa NAPDAC, a jiya ta rufe wasu shaguna 2 a babban birnin tarayya Abuja bisa zargin su da saida kayan da ba’a amince da su bag a yan kasa.
Shagunan suna yankin Zuba da kasuwar Utako.
Mataimakin Daraktan bincike da tantancewa na hukumar Tamanuwa Babab, yace sun gudanar da wannan aikin ne bayan rahotannin da suka dangane da irin kayan da aike saidawa a shagunan.
Dankin gwaje-gwaje na hukumar NAFDAC din ya gano cewa kayan da ake saidawa a shagunan na dauke da wasu sinadarai dake yin illa ga lafiyar dan adam.
Tamanuwa Baba, yace an gano irin wadannan kayan a wani shago da ke yankin Utako.
Ya kuma kara da cewa ana fargarbar kayayyakin sun bazu a kasuwannin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: