Hukumar NCDC tace fiye da mutum 100 ne suka sake kamuwa da cutar Corona

0 76

Cibiyar dakile bazuwar cututtuka ta kasa NCDC Ta bayyana cewa kimanin mutane 105 ne suka kamu da cutar corona, yayin da mutum 3 suka kamu da samfurin Omicron a fadin kasar nan.

NCDC ta bayyana hakan ne a rahotanninta na kullum da take fitarwa a babban birnin tarayya Abuja.

Hukumar ta kuma ja hankalin yan kasar nan akan su kasance masu taka tsan tsan wajan bindokokin kariya daga wannan cutar.

Kawo yanzu dai kimanin mutane dubu dari 214 da 218 ne suka kamu da wannan cutar tin bayan bullarta.

A babban birnin tarayya Abuja ansamu kimanin mutane 16 da suka harbu da cutar sai Jihohin Lagos (43), Gombe (21), Niger (10), Rivers (6), Plateau (5), Edo (2), Bauchi (1), and Kano (1).

A cewar hukumar akwai kimanin mutane 12 da suka warke daga cutar kuma aka sallamesu. Wanda ya mayar da adadin wadanda suka warke daga cutar zuwa dubu dari 207 da dari 304.

Leave a Reply

%d bloggers like this: