Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi daban-daban wadanda jumillar nauyinsu ya kai kilogram sama da dubu 153

0 98

Hukumar NDLEA mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, ta kama kwayoyi daban-daban wadanda jumillar nauyinsu ya kai kilogram sama da dubu 153 da 256.876, cikin mako guda da ya gabata.

Hukumar ta kuma sanar da cewa ta kama mutane 663 da take zargi da laifuka daban-daban cikin makon.

Hukumar ta sanar da haka cikin wata sanarwa da kakakinta, Femi Babafemi, ya fitar jiya a Abuja.

Babafemi yace daga cikin wadanda ake zargi 663 da aka kama, akwai matashi guda mai yiwa kasa hidima, da jami’in dansanda daya da kuma soja guda daya, dukkaninsu da ake kyautata zaton sojojin gona ne.

Yace jami’an hukumar sun kai sumame kan sanannun guraren sayar da kwaya a Lagos da Abuja da Benue da sauran sassan kasarnan a makon daya gabata.

A cewarsa, sumamen ya jawo gano tarun miyagun kwayoyi da nauyinsu ya kai kilogram sama da dubu 153 da 256.879, wadanda aka lalata ko aka kwace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: