Mukaddashin shugaban hukumar shige da fice ta kasa, Immigration, Isa Idris Jere, a yau yayi badda kama a matsayin mai neman fasfon tafiya kasashen waje a ofishin hukumar na Ikoyi a jihar Lagos, inda yayi zargin cewa wasu daga cikin jami’an hukumar sun nemi ya basu cin hanci.

Isa Jere, yayin wata ganawa da manema labarai ta wayar tarho, yace ya yanke shawarar ziyarar bazata cikin bad da kama domin sanin ainihin halin da ‘yan Najeriya ke shiga a hannun baragurbin jami’an hukumar ta Immigration.

Mukaddashin shugaban yace lokacin da ya kama aiki a watan Satumba, yayi alkawarin magance abubuwa uku, dakile kalubalen da ‘yan Najeriya ke fuskanta a yunkurinsu na samun fasfon tafiya kasashen waje, da inganta tsaro a iyakokin kasarnan da kuma inganta jin dadin ma’aikata.

Yace ya kai ziyarar tasa ta bazata zuwa Ikoyi a yau domin tabbatar da zarge-zargen da ake yiwa jami’an hukumar na ofishoshin hukumar dake jihar Lagos da suka hada da Ikoyi da FESTAC.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: