Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa, NEMA, ta fara yakin wayar da kai da shirin tunkarar ambaliya a yankin Doka, Karamar Hukumar Tofa ta Jihar Kano domin rage illar ambaliya yayin daminar shekarar 2025.
Daraktan hukumar, Zubaida Umar, ta ce wannan mataki na daga cikin ajandar “Renewed Hope” ta Shugaba Bola Tinubu da ke nufin inganta ci gaban al’umma da tattalin arziki.
Hukumar NEMA ta samar da taswirar yankuna masu hadari, tare da ƙarfafa hukumomin gwamnati da masu zaman kansu, makarantu da kungiyoyin matasa wajen daukar matakan rigakafi kafin iftila’i ya faru.
Gwamnatin jihar Kano ta ce tana aiwatar da shirin share magudanan ruwa da kuma horar da jami’an agaji a matakin ƙananan hukumomi domin tabbatar da cewa ana da isassun kayan aiki da kudi don dakile ambaliya da sauran ibtila’i.