Hukumar zaben kasar Libya ta cire sunan dan Gaddafi Saif al-Islam,daga cikin wadandsa za su yi takarar shugabancin kasar

Hukumar zaben kasar Libya ta cire sunan dan Gaddafi Saif al-Islam,daga cikin wadandsa za su yi takarar shugabancin kasar a babban zabe da za a watan gobe.
Daurin da aka yi masa a baya na cikin dalilan da aka kafa na daukar wannan mataki.
A 2015 wata kotu a tripoli ta yanke wa Saif al-Islam hukumcin daurin kisa saboda tashin hankalin da ya faru a 2011, rikicin da ya hambarar da gwamnatin mahaifinsa.
Bayan shekaru kokarin Majalisar Dinkin Duniya na ganin an bai wa dimokradiyya mazauni ya kawo karshen yakin basasar.
Za a yi zaben shugaban ƙasa a Libya a ranar 24 ga watan Disamba a karon farko cikin shekara 10.