Hukumar bunkasa addinin musulunci ta jihar Jigawa ta yi kiyasin kashe naira miliyan dubu daya da miliyan dari hudu da saba’in domin gudanar da manyan ayyuka a sabuwar shekara.

Sakataren Zartaswa na hukumar, Dr Abubakar Muhammad Sani, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin hukumar na shekarar 2022 a gaban kwamatin ilimi na majalisar dokokin jihar Jigawa.

Ya ce kasafin kudin zai bada fifiko ga kafa sabbin makarantu da kwaskwarima ga wadanda ake da su tare da gina karin ajujuwa domin bada damar daukar sabbin dalibai da ciyar da wadanda ake da su zuwa ajujuwa na gaba.

Dr Abubakar Muhammad Sani ya bayyana cewa za su gina sabbin bandakuna tare da samar da famfunan tuka-tuka domin inganta samar da ruwan sha ga daliban makarantun Arabiyya.

Ya yi addu’a ga Allah madaukakin Sarki Ya cigaba da yiwa gwamnatin jiha jagoranci wajen aiwatar da kyawawan manufofi da shire-shiryenta tare da fatan kasafin kudin sabuwar shekara zai yi tasiri wajen inganta rayuwar al’ummar nan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: