Gwamnatin Jihar Borno ta raba Kekunan hawa kyauta ga Daliban da suke zaune a karkara domin inganta Ilimin su tare da zuwa Makaranta.

Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum, shine ya gabatar da Kekuna 300 ga Daliban sabuwar Makarantar Sikandiren Fasaha ta Wuyo, bayan ya kaddamar da Makarantar tare da raba kekune kyauta domin inganta ilimin yaran.

Kaddamar da Makarantar na cikin Ayyuka 22 da Gwamnan Jihar ya kaddamar a Kudancin Borno.

Gwamnan Jihar ya ce tsohuwar gwamnatin da ta gabata ce karkashin Jagorancin Kashim Shettima ta siyo kekunan domin samar da Ilimi ga Yaran.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: