Labarai

Hukumomi a Sudan sun ce akalla tumaki dubu 16 suka mutu a ruwa bayan wani jirgin ruwan dakon kaya ya kife a hanyarsa ta zuwa Saudiyya

Hukumomi a Sudan sun ce akalla tumaki dubu 16 suka mutu a ruwa bayan wani jirgin ruwan dakon kaya ya kife a hanyarsa ta zuwa Saudiyya.

Rahotanni sun ce duka bil’adama da ke cikin jirgin sun tsira da rayuwarsu, bayan Jirgin mai na ɗauke da kusan dabbobi dubu 16 ya nutse a kogin bahar rum.

Jami’an tashar ruwa a Sudan ɗin sun bayyana cewa adadin dabbobin da jirgin ya kwasa ya fi ƙarfin adadin da zai iya ɗauka.

Kasar Sudan da tasha fama da matsin tattalin arziki saboda juyin mulkin daya gudana a watan Oktoban bara, itace kasa mafi arzikin dabobi a nahiyar Afrika, wanda mafi yawanci kasashen Misra da gabas ta tsakiya ne manyan abokan huldar cinikayyarsu.

Wata majiya da bata bayyana kanta ba tace lamarin ya haifar da asarar sama da riyal miliyan 15 na kasar saudiyya.

Wannan dai na zuwa ne dai-dai lokacin da ake matuƙar buƙatar tumaki a Saudiyya ganin cewa miliyoyin Musulmi za su yi layya a Babbar Sallah mai zuwa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: