Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya saki fursunoni 40 tare da sassauta hukuncin kisa guda shida zuwa daurin rai da rai, albarkacin ranar demokradiyya.

Ya ce an yi hakan ne domin murnar zagayowar ranar Dimokuradiyya da kuma bukatar rage cunkoso a cibiyoyin gyaran da’a a fadin jihar.

Abiodun ya bayyana hakan ne a jawabinsa a taron ranar dimokuradiyya da aka gudanar a filin wasa na Moshood Abiola dake Abeokuta, babban birnin jihar.

Gwamnan ya kuma jinjinawa MKO Abiola, wanda ake kyautata zaton ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993.

A cewarsa, babu wata fa’ida cewa fafutukar da aka yi a ranar 12 ga watan Yuni kamar yadda MKO ya shirya ta haifar da dimokuradiyyar da muke fama da ita a yanzu a Najeriya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: