Idan an daddale, zamuyi gwanjon gwala-gwalai, sarƙoƙi, awarwaro na Dala Miliyan 40 – Shugaban EFCC

0 147

Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya bayyana cewa har yanzu EFCC ba ta kai ga kaɗa ƙararrawa ta yi gwanjon gwala-gwalan da ta kama a hannun Diezani, tsohuwar Ministan Harkokin Fetur ba, saboda har yanzu kai-kawon daddale komai da komai na daga dukiyar gwala-gwalan tukunna.

Bawa ya yi wannan bayani a gaban Kwamitin Majalisar Tarayya mai binciken abin da ake yi da kuɗaɗen satar da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke ƙwatowa.

Cikin watan Yuli 2019 ne Babbar Koli ta Lagos ta bayar da iznin ƙwace dukkan gwala-gwalan da EFCC ta ƙwato daga hannun Diezani, waɗanda sun kai kwatankwacin dala miliyan 40.

Sarƙa Da Awarwaron Sata Na Dala Miliyan 40:

1. ‘Yan-hannu ‘set’ 419.
2. ‘Yan-kunne guda 304,
3. Zobba guda 325.
4. Agogunan kece raini guda 189.
5. Sarƙa guda 267.
6. Wata tsaleliyar waya ta gwal, mai tsadar gaske.

Yayin da Bawa ya koma Majalisa a ranar Juma’a, kwamiti ya kulle ƙofa tare da Bawa, inda ya yi masu ƙarin bayani kan wasu kuɗaɗen da aka yi hada-hadar su bisa tsari na tsaro.

Amma da aka dawo zauren zaman bincike, Bawa ya shaida wa kwamiti cewa baya ga gwala-gwalai na dala miliyan14.14 da aka ƙwato hannun Diezani, an kuma ƙwato kadarorin da su ka hada da gidaje da motoci har na dala miliyan 80.

Sbugaban Kwamiti Adejoro Adeogun ya tambayi Bawa dalilin jinkirin yin gwamjon kadarorin.

Shi ne Bawa ya ce masa kai-kawon tsarin aiki da jeƙala-jeƙalar zuwa kotu ne su ka kawo jinkirin.

Adeogun ya ce kwamitin sa zai kafa karamin kwamiti domin ya je Hukumar EFCC a ga yanayin da kadarodin ke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: