INEC Ta Duƙufa wajen Gano Kurakuran Zaɓen 2019 Domin Gyara A 2023

0 182

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta ce duba matsalolin da aka fuskanta yayin zaben 2019 da ya gabata zai taimaka wajen samun gyare gyare a babban zaben 2023 dake tafe.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Mr. Fetus Okoye ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kaduna, inda ya ce duba matsalolin da aka fuskanta yayin zabe 2019 zai taimaka matuka wajen tunkarar zaben 2023.

Okoye ya ce hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa zata yi aiki da majalisar dattawa domin samun managartan tsare tsare akan zaben dake tafe cikin 2023.

Ya kara da cewa hukumar har ila yau tana duba rahoton da masu sa ido kan zabe na cikin gida da kuma na kasashen waje suka gabatar kan zaben 2019.

Leave a Reply

%d bloggers like this: