Iran Ta Sake Bude Ofishin Jakadancinta A Saudiyya, Bayan Shekaru Bakwai Da Yanke Huldar Diflomasiyya

0 93

Iran ta sake bude ofishin jakadancinta a Saudiyya, shekaru bakwai bayan da masu hamayya da juna a yankin suka yanke huldar diflomasiyya.

Wakilan ma’aikatar harkokin wajen Iran da na Saudiyya sun halarci bikin a Riyadh babban birnin kasar Saudiyya.

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Alireza Bigdeli, ya ce wannan alama ce da ke nuna an shiga wani sabon matsayi na hadin gwiwa

Hakan dai na zuwa ne watanni uku bayan da kasashen yankin Gulf suka amince da maido da alakar, a zaman yarjejeniyar da China ta shirya.

A shekarar 2016 ne Saudiyya ta yanke hulda da kasar Iran bayan harin da aka kai wa ofishin jakadancinta da ke Tehran babban birnin kasar Iran, sakamakon zanga-zangar adawa da hukuncin kisa da Saudiyya ta yi wa wani fitaccen malamin Shi’a. A wata ganawa da ya yi da takwaransa na Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan Al Saud a ranar Juma’ar da ta gabata a kasar Afirka ta Kudu, ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian ya bayyana gamsuwa da ci gaban da aka samu a huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: