Kungiyar wasan kwallon kafa Enyimba ta lashe kofin gasar Firimiya ta Najeriya karo na tara bayan da ta yi kunnen doki da Rivers United a filin wasa na Mobolaji Johnson Arena da ke Onikan a Legas a daren jiya.
Tawagar Finidi George ta kare a matsayi na daya da maki tara a wasanni biyar a gasar manya kungiyoyi guda shida.
Kungiyar ta Aba ta kuma samu gurbi a gasar cin kofin zakarun nahiyar Africa a kakar wasa mai zuwa.
A halin da ake ciki kuma, kungiyar Al Ahly ta kasar Masar ta lashe gasar zakarun nahiyar Afrika karo na 11.
Al Ahly ta tashi kunnen doki 1-1 da Wydad Casablanca a wasan karshe na zagaye na biyu a Morocco, inda ta samu nasara da ci 3-2 a wasanni biyun.
Wydad Casablanca ta doke abokiyar hamayyarta Al Ahly a gasar ta bara a birnin Casablanca.