Za a gurfanar da jami’an ‘yan sanda shida a kasar Switzerland bisa zargin kisan gilla kan mutuwar wani dan Najeriya

0 125

Za a gurfanar da jami’an ‘yan sanda shida a kasar Switzerland bisa zargin kisan gilla kan mutuwar wani dan Najeriya mai suna Mike Ben Peter shekaru biyar da suka gabata.

Mike Ben Peter ya mutu bayan an kama shi a birnin Lausanne.

‘Yan sanda sun ce sun yi amfani da dabarun da suka dace wajen cafke wanda ake zargi da sayar da muggan kwayoyi.

Jami’an ‘yansanda sun take wuyansa a kasa bayan ya ki a bincike shi.

Lauyoyin wanda ake kara za su kafa hujja da cewa mutuwar Mike Ben Peter na iya kasancewa sakamakon matsalolin rashin lafiya. Iyalan mamacin da kungiyoyin masu adawa da wariyar launin fata a Switzerland sun kwatanta kisan da na George Floyd, wanda ‘yan sanda suka kashe a Minneapolis a kasar Amurka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: