Iran za ta kai hare-hare a kan muhimman kadarorin Isra’ila

0 117

Iran ta ce za ta kai hare-hare a kan “muhimman kadarorin” Isra’ila idan har ta mayar mata da martani.

Babban hafsan tsaron Iran, Manjo Janar Mohammad Bagheri ne ya yi wannan gargaɗin, inda ya yi barazanar ƙaddamar da hare-haren da zarar Isra’ila ta ce musu kule.

“Idan Isra’ila ta ta cigaba da hare-haren da take yi, ko kuma ta nemi ta taɓa mutuncinmu da ƴancin ƙasarmu, lallai za mu maimaita irin waɗannan hare-haren da muka yi, ko kuma ma waɗanda suka fi zafi domin za mu kai hare-haren ne a kan dukkan kadarorinta,” in ji Bagheri.

Ya ce dakarun Iran Revolutionary Guard Corps a shirye suke domin kare ƙasar, da kuma maimaita irin hare-haren da suka kai a daren Talata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: