Sama da mutum 90 aka tabbatar sun mutu sakamakon guguguwar Helene

0 78

Sama da mutum 90 aka tabbatar sun mutu a sassan Amurka sakamakon guguguwar Helene da ke tafe da iska da ruwan sama mai karfin gaske.

Hukumomi sun ce a North Carolina kadai mutane sama da 30 ne suka rasa rayukansu.

Guguwar tafe da tsawa ta tafka ta’adi sosai a jihohin Florida da Georgia. Akwai kuma birane da dama da tittunan da suka lalace sakamakon ambaliya, haka kuma akwai milyoyin mutane da lantarkinsu ya katse.

Shugaba Biden ya ce zai ziyarci wasu daga cikin yankunan da suka fuskanci wannan iftila’i

Leave a Reply

%d bloggers like this: