Hukumar Samar da Guraben Karatu a Makarantun Gaba da Sakandire (JAMB) zata iya gudanar da jarabawa shiga makarantun gaba da sakandire karo na biyu a bana, domin daliban da suka fuskanci kalubale na hakika wajen yin rijista.

Magatakardar hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede, ya sanar da haka jiya a Lagos lokacin da yake duba yadda ake daukan sunayen daliban da suka fuskanci matsalar data hana su yin rijistar jarabawar.

Ya nanata jajircewar hukumar wajen tabbatar da cewa dukkanin yan Najeriyan dake bukatar yin karatun gaba da sakandire, an basu cikakkiyar dama.

A cewar magatakardar, wasu daliban sun fadi gaskiya cewa basu da kudaden sayen takardun rijistar jarabawar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: