Wani dan majalisar wakilai na tarayya daga jihar Kebbi, Kabir Ibrahim Tukura, ya gayawa abokan aikinsa a jiya cewa sama da mutane 500 aka kashe, aka sace 201 tare da raba dubu 15 da gidajensu a hare-haren yan fashin daji akan kauyukan manoma dake kananan hukumomin Sakaba da Danko/Wasagu na jihar.

Sai dai, bai bayyana lokacin da wadannan hare-haren suka auku ba.

Kazalika, bai mayar da martani ba, bayan manema labarai sun nemi yayi karin haske.

Dan majalisar yace rahotanni sun yi nuni da cewa kimanin shanu dubu 5 da tumakai dubu 3 aka sace a yankunan cikin mako guda kacal da ya gabata.

Yace maharan na tafiya a garuruwansu daga gari zuwa gari, suna neman shanun da zasu sace, da kayan abincin da za suyi awon gaba da shi, tare da mutanen da za suyi garkuwa da su.

Da take amincewa da kudirin, majalisar ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika da karin jami’an tsaro zuwa yankin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: