Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya amince da sake nadin Abdul’aziz Abdulhamid a matsayin shugaban hukumar amintattu na asusun adashen gata na Fansho na jiha da kuma kananan hukumomi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren gwamnatin jiha, Adamu Abdulkadir Fanini ya sanyawa hannu.

Haka kuma gwamnan ya amince da nadin Alhaji Garba Muhammad Auyo da Injiniya Nasiru Mahmoud Babura da Sarki Baba Jahun a matsayin wakilan hukumar amintattu na asusun adashen gata na fansho na jiha da kuma kananan hukumomi.

Sanarwar ta kara da cewar sauran wakilan hukumar amintattun sun hadar da shugaban kungiyar kwadago na jiha da shugaban kungiyar Malamai da shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi da sauransu.

Kazalika, Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya amince da nadin Habibu Muhammad Ringim a matsayin mataimaki na musamman ga gwamna kan bunkasa shirye-shirye gwamnati a kafafan yada labarai.

Sanarwar ta kara da cewar nadin ya fara aiki nan take.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: