Donald Trump ya yabawa Najeriya kan dakatar da shafin sada zumunta na Twitter.

0 79

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya yabawa Najeriya kan dakatar da shafin sada zumunta na Twitter a kasarnan.

A wata sanarwa da shugaban ya fitar ya ce yana yi wa Najeriya murna bisa haramta amfani da Twitter saboda shafin ya haramtawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari amfani da shi.

Sai dai Twitter bai haramta wa Shugaban Buhari amfani da shafin ba, illa dai ya cire wani sakon ne da shugaban kasar ya wallafa kan masu kokarin raba kasarnan, sannan ya dakatar da shugaban kasar tsawon awa 12.

Haka kuma, Donald Trump ya yi kira ga sauran kasashe da su bi sawun Najeriya wajen takaitawa ko haramta amfani da Twitter da Facebook.

An haramtawa Donald Trump amfani da Twitter da Facebook tun a watan Janairu bayan an zarge shi da wallafa sakonnin da suka tunzura magoya bayansa zuwa majalisar Amurka. Mutane 5 ne suka mutu a lamarin.

A jawabinsa, Donald Trump yace a lokacin mulkinsa yayi tunanin haramta amfani da Facebook da Twitter a kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: