NECO tace har yanzu ranar 25 ga watan Yuni ce ranar karshe ta yin rajistar jarabawar SSCE

0 68

Hukumar shirya jarabawar ta kasa (NECO) tace har yanzu ranar 25 ga watan Yuni ce ranar karshe ta yin rajistar jarabawar kammala makarantar sakandare (SSCE).

Wata sanarwa da hukumar jarrabawar ta fitar yau dauke da sa hannun shugaban ta na yada labarai da bangaren hulda da jama’a, Azeez Sani, ta bukaci masu ruwa da tsaki da abin ya shafa da suka hada da ma’aikatun ilimi na jihoshi, da masu makarantu da sauransu, da su tabbatar da kiyaye wa’adin.

Sanarwar ta yi bayanin cewa aikin rajistar wanda aka fara a ranar 31 ga Maris, za’a rufe ne a ranar Juma’a, 25 ga Yuni, 2021 kuma ba za a daga ba, yayin da za’a fara rubuta jarabawar babu kama hannun yaro, a ranar Litinin, 5 ga Yuli, 2021.

Hukumar ta NECO tace an dauki matakin ne da nufin samar da ingantaccen tsari da samar da kayan aiki na jarabawa wanda ake bukata domin gudanar da jarrabawar cikin sauki.

Sanarwar ta bukaci masu ruwa da tsaki da su tabbatar sun kammala rajistar dalibansu a kan lokaci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: