Rundunar Yan sandan Jihar Kaduna, ta kubutar da mutane 5 daga hannun wasu yan bindiga

0 82

Rundunar Yan sandan Jihar Kaduna, ta kubutar da mutane 5 daga hannun wasu yan bindigar wanda sukayi garkuwa da su a kananan hukumomin Jema’a da Igabi na Jihar.

Kakakin rundunar SP Muhammad Jalige, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, inda ya ce sun kubutar da mutanen ne a lokacin da suke kokarin tserewa da mutanen a hanyar Jagindi Godo-Godo ta karamar hukumar Jema’a.

A cewarsa, bayan samun faruwar lamarin ne Shugaba Ofishin yan sanda na Karamar hukumar Kafanchan, ya jagoranci yan sanda domin kubutar ra mutanen.

A wani labarin kuma, rundunar yan sandan jihar Kaduna sun kubutar ta wata Mata da yarta wanda yan bindigar sukayi garkuwa da su a yankin Rigasa ta karamar hukumar Igabi.

Manema labarai sun rawaito cewa yan sanda, sun samu rahoton cewa yan bindiga sun kewaye gidan Abdulganiyu Husseini Mahuta, tare da yin garkuwa da Matarsa da kuma Yarsa.

Bayan fafatawa a tsakaninsu, yan sanda sunyi nasarar kubutar ta Matar tasa da yarsa, sai dai kuma sunyi awun gaba da Mai gidan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: