Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun yi awon gaba da wani Jigo a Jam’iyar PDP Mai suna Hamidan Habu a Karamar Hukumar Ringim ta nan Jihar Jigawa.

Wata Majiya data bukaci a sakaya sunanta, ta fadawa menama labarai cewa, yan bindigar sunje gidan mutumin ne da misalin karfe 1:30 na dare a kyauyen Shangel dake karamar hukumar Ringim.

Majiyar ta ce bayan yan bindigar sunje gidan mutumin ne, sunyi harbe-harben Iska tare da yin awun gaba dashi.

Mutanen garin sunyi kokarin kubutar da mutumin, amma hakan ya Gagara, saboda harbe-harben da sukayi domin tsoratar da mutanen.

Kakakin ’yan sandan Jihar Jigawa, ASP Lawan Shisu ne ya tabbatar da hakan a Dutse a safiyar yau Laraba.

A cewarsa, a ranar 6 ga Yuni da misalin karfe 1:30 na dare, wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun sace Hamidan Habu mai shekara 55, a kauyen Shengel da ke Ringim zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Kakakin ya ce Sai da suka yi harbe-harbe a iska kafin su tafi da shi daga kauyen da ke da nisan kilomita 25 da garin Ringim.

Daga baya jami’an ’yan sanda sun ziyarci wurin da lamarin ya faru, inda suka gano fankon harsashi.

A cewar kakakin, ’yan sandan na ci gaba da bincike tare da bin sahun wadanda suka yi awon ga a da mutumin don cafke su.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: