Jami’ar Khadijah Majia ta jihar Jigawa ta fara shiryen-shiryen daukan sabbin dalibai na zangon karatu na 2022 zuwa 2023

0 86

Jami’ar Khadijah dake garin Majia a karamar hukumar Taura ta jihar Jigawa ta fara shiryen-shiryen daukan sabbin dalibai na zangon karatu na 2022 zuwa 2023.

Mataimakiyar Shugabar Jami’ar Farfesa Hassana Sani Darma ta bayyana haka ta cikin wani shirin Radio Jigawa.

Hassana Darma ta shawaraci wadanda suke sha’awar shiga jami’ar su kasance sun samu maki 140 a jarrabar shiga Jami’o’i da manyan makarantu ta JAMB da kuma credit 5 a darusan Turanci da Lissafi da sauran darussa 3 masu alaka da kwas din da za a karanta.

Ta kara da cewa daliban da suka mallaki takardar kammala NCE da Diploma da kuma IJMB zasu samu gurbin karatu kai tsaye na DE.

Mataimakiyar shugabar jami’ar ta ce tuni jami’ar ta samar da ingantattun kayayyakin koyo da koyarwa a dukkanin tsangayoyin karatu guda uku dake jami’ar tare da kwararrun malamai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: