Jami’ar Tarayya ta Dutse ta dauki mafarauta guda 55 aikin kare rayuka da dukiyoyi a harabar jami’ar da kewaye

0 81

Jami’ar Tarayya ta Dutse (FUD) ta dauki mafarauta guda 55 aikin kare rayuka da dukiyoyi a harabar jami’ar da kewaye.

Babban jami’in yada labarai na jami’ar, Abdullahi Yahaya, ya sanar da hakan a jiya a wata sanarwa da ya fitar a birnin Dutse.

Abdullahi Yahaya ya ce mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Abdulkarim Sabo Muhammad, ya amince da daukar mafarautan yankin.

Ya bayyana cewa an zabo su ne daga kungiyar mafarauta ta kasa reshen jiharnan.

A cewar Abdullahi Yahaya, matakin zai taimaka wajen bayar da isasshen taimako ga sashin tsaro na jami’ar wajen sintiri a harabar jami’ar, musamman da daddare.

Ya ambato mataimakin shugaban jami’ar na cewa jami’ar na bukatar ayyukan mafarauta ne saboda dimbin ilimin da suke da shi a cikin al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: