Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Kasa, NNPC, Mele Kyari, ya bayyana cewa za a iya siyar da litar Man Fetur tsakanin Naira 320 zuwa 340 a shekara mai zuwa ta 2022.

Mele Kyari, wanda ya sanar da haka a jiya yayin da yake gabatar da jawabi a taron bunkasa ci gaban Najeriya na Bankin Duniya, Abuja, ya ce hakan ya faru ne saboda doka ba ta tanadi tallafi ba, don haka za a cire shi a shekara mai zuwa.

A cewarsa, dokar ta tanadi cewa ya zuwa karshen watan Fabrairun 2022, ya kamata a cire tallafin man fetur a kasarnan.

Dangane da hauhawar farashin iskar gas, ya ce lamarin yazo ne saboda ana fama da matsalar iskar gas a duniya kuma kasashe da dama na fuskantar barazanar rashin gas a watan Disamba.

Mele Kyari, ya bayar da tabbacin cewa kamfanin yana aiki don habaka abubuwan da ake samarwa a cikin gida don biyan bukatun masu amfani.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: