Jam’iyar APC ta ce zata yi farin ciki Idan tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya koma jam’iyyar

0 58

Jam’iyar APC ta ce zata yi farin ciki Idan tsohon Shugaban Kasa Dr Goodluck Jonathan, ya yanke shawarar komawa cikin Jam’iyar mai Mulki.

Sakataren Jam’iyar Sanata John James Akpanudoedehe, shine ya bayyana hakan a lokacin da ya bayyana a gidan Talabijin na Channels Tv ta cikin shirin Politics Today, a jiya Laraba, inda ya ce shigowar Jonathan cikin Jam’iyar zai sake karfafata.

Amma bai amsa tambayar da aka masa ba, kan cewa ko Jam’iyar zata bashi takarar kujerar Shugabancin Kasa, idan ya koma Jam’iyar.

A cewarsa, Jam’iya mai mulki tana da wani tanaji data yiwa wadanda suke shawa’ar komawa cikin ta, ciki harda basu dukkan wani mukamin gwamnati.

A daidai lokacin da zaben shekarar 2023 ke kara karatowa, wasu na ganin tsohon Shugaban Kasar zai iya komawa Jam’iyar APC kuma ana ganin zai iya samun tikitin kujerar takarar shugaban kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: