Gwamnatin Tarayya ta sake jadadawa ‘yan Najeriya cewa tana dab da dage haramcin daina amfani da shafin Tuwita

0 71

Gwamnatin Tarayya ta sake jadadawa ‘yan Najeriya cewa tana dab da dage haramcin daina amfani da shafin Tuwita a fadin kasar nan bada jimawa ba.

Ministan labarai da raya al’adu, Lai Mohammed ya tabbatar da hakan ne a lokacin amsa tambayoyin ‘yan jarida a fadar gwamnati, bayan taron majalisar zartarwa a Abuja.

Sai dai ministan bai sanar da hakikanin ranar dage haramcin ba, ko ranar da za a koma amfani da shafin, amma yace tattaunawa tsakaninsu da masu shafin na tafiya babu cikas cikin mutuntawa.

A jiya aka cika kwana 100 da haramcin daina amfani da Tuwita, bayan da gwamnati ta yi zargin cewa ana amfani da shafin wajen kokarin tarwatsa kasar ta hanyar yada labaran karya da ke iya haddasa tashe-tashen hankula.

Lai Mohammed a ranar 9 ga watan Yuni ya lissafa sharruda 9 da dole Twitter ta cika, da suka hada da yin rijista a matsayin kamfani a Najeriya.

Akwai rahotannin dake cewa Najeriya ta tafka asarar naira miliyan 148 saboda haramta amfani da Twitter.

Leave a Reply

%d bloggers like this: