Wakilan hukumomi sun ziyarci wurare 2 da ake saran gina Jami’ar Fasaha ta tarayya dake Babura

0 94

Wakilan Gwamnatin tarayya daga Ma’aikatar Ilimi da kuma Hukumar Kula da Jami’oi ta Kasa NUC sun ziyarci wurare 2 da ake saran gina Jami’ar Fasaha ta tarayya dake Babura.

Idan za’a iya tunawa de a watan Yuli ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa Jami’ar Fasaha ta tarayya a Babura, tare da Kafa Kwamatin Fasaha wanda zasu tantance wuraren da za’a gina Jami’ar.

Wuri na farko da ake tunanin gina Gina Jami’ar shine hanyar Kano daga Babura, inda kuma wuri na biyu ya kasance Kwalegin Share Fagen Shiga Jami’a da ke Babura, inda ake saran mayar da Makarantar zuwa Jami’ar Fasaha.

Ziyartar wurin na nufin wani shirye-shiryen da gwamnati take yi domin fara aiwatar da ginin Jami’ar.

Gwamnan Muhammadu Badaru Abubakar, da Kwamishinan Ilimi na Jiha Dr Lawan Yunusa Danzomo, da Kwamishinan Kasa da Safiyo Sagir Musa Ahmed da kuma Babban Sakatare a Ma’aikatar Lafiya Dr Salisu Mu’azu na daya cikin wadanda suka yiwa Wakilan gwamnatin tarayya rakiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: