Gwamnan Jihar Bauchi ya nada sabon Shugaban Ma’aikata na Jihar

0 112

Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad, ya nada Alhaji Yahuza Haruna, a matsayin sabon Shugaban Ma’aikata na Jihar.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da kakakinsa Mukhtar Gidado, ya sanyawa hannun kuma aka rabawa manema labarai a birnin Bauchi.

A cewarsa, nadin nasa ya biyo bayan ritayar da shugaban Ma’aikata na Jiha Aliyu Jibo ya yi daga aiki.

Sanarwar ta ce Gwamna Bala Muhammad, ya godewa Alhaji Aliyu Jibo, bisa yadda ya sadaukar da kansa a wurin yiwa jihar Hidima har zuwa lokacin ritayarsa.

Kafin nadin sabon Shugaban Ma’aikatan, Alhaji Yahuza Haruna, shine babban sakatare a ma’aikatar Kasafi da tattalin arzikin Jihar.

Kazalika, sanarwar ta ce gwamna Bala Muhammadu ya amince da nadain sabbin  manyan sakatarorin ma’aikatu 22.

Leave a Reply

%d bloggers like this: