UNICEF: Akwai yiwuwar yara miliyan daya a Najeriya su daina zuwa makaranta saboda barazanar sace su

0 117

Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce akwai yiwuwar yara miliyan daya a Najeriya su daina zuwa makaranta saboda barazanar da suke fuskanta ta sace daliban makarantu da aka yi a kasar a wannan shekara.

A ranar Laraba Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wannan sanarwa inda ta ce, ‘yan bindiga sun sace sama da yara 1,436 a makarantu domin karbar kudin fansa a Najeriya tun daga watan Disamba yayin da wasu da dama suke hannu har yanzu.

Asusun ba da tallafin ƙananan yara na UNICEF ya ce an kai hare-hare 20 kan makarantun Najeriya a wannan shekarar kuma an saci yara 1,400, yayin da aka kashe 16.

An saki mafi yawan cikinsu bayan biyan fansa bayan kwashe makwanni ko kuma watanni a hannun ‘yan fashi, inda ake ajiye su a wasu sansanonin da ake yi a dazuka.

UNICEF ya ce kimanin Yara Miliyan 37 ne suka fara karatu a cikin watan nan, kuma kimanin Yara miliyan 1 ne aka bari a baya saboda matsalar tsaro.

Shugaban UNICEF na Najeriya Mista Peter Hawkins, ya bayyana damuwarsa kan yadda ake barin yaran a baya, duk da rin kokarin da gwamnati take yi.

Kazalika, ya ce kawo karshen matsalar tsaron shine mafita kan matsalar da Yaran suke ciki a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: