Sen. Ali Modu Sheriff ya gana da Gwamna Badaru domin neman goyan bayan sa kan kudurinsa

0 119

Tsohon Gwamnan Jihar Borno Sen. Ali Modu Sheriff ya jagoranci wata tawaga inda suka gana da Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar domin neman goyan bayan sa kan kudurinsa.

An rawaito cewa Sen. Ali Modu Sheriff, ya fadawa Gwamna Badaru Abubakar nufinsa na neman kujerar Shugaban Jam’iyar APC na Kasa, matukar za’a tura kujerar zuwa yankin Arewa Maso Gabas.

Cikin mutanen da suka raka Sen. Ali Modu Sheriff zuwa gun Gwamna Badaru sun hada da Dr Cairo Ojugbo wanda jigo ne a Jam’iyar da sauran kusoshin Jam’iyar.

Ziyarar da Sen. Ali Modu Sheriff ya kaiwa Gwamna Badaru Abubakar, ya nuni da cewa wata manufa ce ta Sen. Ali Modu Sheriff na neman kujerar shugaban Jam’iyar na Kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: