Labarai

Jam’iyar NNPP ta karyata rahotannin da suke cewa Kwankwaso zai yiwa dan takarar jam’iyar Labour Party Peter Obi mataimaki a zaben 2023

Jam’iyar NNPP ta karyata rahotannin da suke cewa Dan Takarar ta na shugaban Kasa Engineer Rabiu Musa Kwankwaso, zai yiwa Dan Takarar Jam’iyar Labour Party Mista Peter Obi, mataimaki a zaben 2023.

Cikin wata sanarwa da Sakataren Jam’iyar Mista Agbo Major, ya sanyawa hannu, ya bayyana cewa babu wani lokaci da aka taba yin irin wannan maganar a Zahiran ce.

A cewarsa, Jam’iyar NNPP bata taba shakkar tsayar da Rabiu Engineer Musa Kwankwaso, a matsayin dan takarar ta ba, saboda haka babu yadda za’ayi ya yiwa Peter Obi mataimakin a Jam’iyar Labour Party.

Sanarwar ta ce labarin da ake yadawa wani yunkuri ne na ruda mutane, tare da kaskantar da Jam’iyar da kuma dan takarar ta, Sanata Kwankwaso, wanda yake da Miliyoyin masoya a kasa da waje.

Mista Agbo, ya bukaci yan Jarida su rika tantance labaran su kafin yadawa domin kawar da fitina a shirye-shiryen zabe mai zuwa na 2023.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: