A ranar Talata ne majalisar dattawa ta nada Sanata Philip Tenimu Aduda (FCT) a matsayin sabon shugaban marasa rinjaye na majalisar. Haka kuma an nada Sanata Chukwuka Utazi a matsayin bulaliyar marasa rinjaye a majalisar dattawa.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne ya sanar da nadin yayin da yake karanta wasiku daban-daban guda biyu dauke da sa hannun sakataren jam’iyyar PDP na kasa Samuel Anyanwu.

Kujerar Shugaban Marasa Rinjaye ta zama babu kowa a kanta tun bayan ficewar Sanata Enyinnaya Abaribe (Abia ta Kudu) daga PDP.

-Legit Hausa

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: