Labarai

Yan bindiga sun kashe wani makiyayi mai suna Ado Mamman a kyauyen Pai da ke karamar hukumar Kwali ta birnin tarayya Abuja

Yan bindiga sun kashe wani Makiyayi mai suna Ado Mamman, a kyauyen Pai da ke karamar hukumar Kwali ta birnin tarayya Abuja.

Wani mazaunin garin Pai mai suna Shehu, ya fadawa manema labarai cewa yan bindigar sun je garin ne da misalin karfe 11:12 na Daren Jiya.

A cewarsa yan bindigar sun shiga garin ne dauke da manyan bindigogi a lokacin da mazauna garin suke kokarin kwanciya.

Majiyar ta ce yan bindigar sun harbi Marigayin a kirgi a lokacin da yake kokarin hanasu tafiya da dan uwansa mai suna Maude Ado.

Sakataren Kungiyar Miyatti Allah na Karamar Hukumar Gwagwalada Malam Muhammad Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma kashe mutumin a garin na Pai.

Haka kuma ya ce an binne Marigayin a yau da safe kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Kakakin rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja DSP Adeh Josephine, bata amsa kira da sakon text message din da aka tura mata ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: