Jam’iyar PDP ta karbi mambobin jam’iyyar APC kimanin 670 wanda suka sauyin sheka a karamar hukumar Gagarawa ta nan Jihar Jigawa

0 295

Jam’iyar PDP ta karbi Mambobin Jam’iya mai Mulki ta APC su kimanin 670 wanda suka sauyin sheka a karamar hukumar Gagarawa ta nan Jihar Jigawa.

Shugaban Jam’iyar PDP na Jihar Jigawa Hon Babandi Ibrahim Gumel shine ya karbi masu sauyin shekar.

Daga cikin sauyan Yayan Jam’iyar PDP da suka halarci taron masu sauyin shekar sun hada da Hon. Bashir Adamu Jumbo, Hon. Nasir Mohammed Sparrow, Hon. Nasiru Umar Roni da kuma Shugaban Matasa na Jam’iyar PDP na Jiha Hon Kabiru Kazaure.

Da yake Jawabi a madadin wanda suka bar Jam’iyar APC, Shugaban Masu Sauyin Shekar Alhaji Tanimu Maitsintsiya, ya bayyana cewa sun amince su bar Jam’iyar APC ne saboda gazawarta wajen cika Alkawarikan da ta dauka a lokacin yakin neman zabe, wanda hakan ne yasa suka koma PDP.

Leave a Reply

%d bloggers like this: