Akalla mutane 10 ne suka mutu sakamakon hadarin Mota a karamar hukumar Garki ta nan Jihar Jigawa.

Mutanen 10 sun mutu ne a sanadiyar hadarin motar da ya faru a kyauyen Dadin Duniya na karamar hukumar ta Garki.

Wani shaidar gani da Ido mai suna Ibrahim Shehu, ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai, inda ya ce hadarin ya faru ne  tsakanin wata Mota kirar Honda UK da kuma Golf Wagon, inda suka kokarin wuce juna.

A cewarsa, Motar Honda Uk ta fito ne daga Garki da nufin zuwa Kano, inda ita kuma Golf Wagon din wanda ta dauko fasinjoji ta fito ne daga Kano zuwa Gumel lokacin da lamarin ya faru.

Jami’in Yada Labarai na karamar hukumar Garki, ya ce cikin mutanen da suka Mutu a hadarin sun hada da Malam Abdullahi wanda Malami ne a Sashen Nazarin Halintu na Jami’ar Bayero ta Kano, da kuma Direban Shugaban Karamar Hukumar Garki Malam Nasiru Yusif.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: