Rundunar Yan Sandan Jihar Katsina ta yi Holon Mista Bishir Hayatu, mutumin da aka zargi da sace wata Mota Toyota Hilux mallakin gwamnatin Jihar Katsina.

Mutumin mai shekara 32 an kamashi ne a ranar 27 ga watan Agustan daya gabata a kyauyen Dayi na karamar hukumar Malumfashi ta Jihar, a lokacin da yake kokarin kaiwa Motar zuwa Abuja domin sayarwa.

Kakakin rundunar yan Sandan Jihar Katsina SP Gambo Isah, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake holon Barawon, inda ya ce mutumin ya kwaran ce wajen Iya satar Motoci a Jihar.

A cewarsa, Motar da aka sace mai Lamba KT 76 B01 mallakin gwamnatin jihar Katsina ce karkashin Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Dr Mustapha Inuwa.

Haka kuma ya ce a watannin baya, an taba kama mutumin da irin wannan laifin na satar Mota.

Kazalika, ya ce a lokacin da ake bincikar sa, Mutumin ya amsa cewa shimai kasuwancin Motoci ne fiye da shekaru.

Sai dai ya musanta zargin dake cewa ya sace Motar ne.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: