Jam’iyyar APC a jihar Jigawa tace ayyukan cigaban da ta gudanar a yanzu sun isa su sanya ta lashe zabe a shekarar 2023

0 81

Jam’iyyar APC a jihar Jigawa a jiya tace ayyukan cigaban da ta gudanar cikin shekaru 6 da suka gabata, sun isa su sanya ta lashe zabe a shekarar 2023.

Shugaban jam’iyyar na jiha, Aminu Sani, ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a Dutse.

Aminu Sani ya nanata cewa jam’iyyar APC kasancewar ta cika dukkan alkawarukan da ta dauka yayin yakin neman zabe a 2015 da 2019 a fadin kasarnan, za ta cigaba da zama wacce jama’a ke marawa baya.

Shugaban ya bayyana cewa jam’iyyar APC a jihar Jigawa a karkashin gwamnatin Gwamna Muhammad Badaru ta yi nasarar aiwatar da akalla wani aiki daya a kowace mazaba a kananan hukumomi 27 na jihar.

Aminu Sani ya ce daga shekarar 2015 zuwa yau gwamnatin jihar ta tallafa wa matasa sama da dubu 250 da suka hada da matan aure ta hanyar tsare-tsare daban-daban a kokarin da take na kawar da fatara da samar da arziki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: