Gidauniyar Coca-Cola da Whitefield zasu bayar da jari ga mata da matasa dubu 20 a jihar Kano

0 92

Gidauniyar Coca-Cola, tare da hadin gwiwar gidauniyar Whitefield, zasu bayar da jari ga mata da matasa dubu 20 a jihar Kano.

Da take jawabi a wajen kaddamar da shirin a jiya, babbar jami’ar gidauniyar WhiteField, Fummi Johnson, ta ce akwai wani shiri na bayar da jari ga matasan Najeriya dubu 60, daga ciki aka ware dubu 20 ga jihar Kano.

A cewarta, ya zuwa yanzu kungiyoyin biyu masu zaman kansu sun tallafa wa mata da matasa dubu 87 da 260 a fadin kasar nan.

Ita ma da take jawabi, Daraktar Hulda da Jama’a da Sadarwa ta kamfanin Coca-Cola a Najeriya, Nwamaka Onyemelukwe, ta ce tun da aka kafa gidauniyar Coca-Cola a shekarar 1984, ta kashe sama da dala biliyan 1.2 wajen tallafawa mutane a fadin duniya.

Tun da farko a nasa jawabin kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kano Kabiru Ado Lakwaya ya yaba da shirin, inda ya ce hakan zai taimaka wa gwamnatin jihar a yunkurinta na samar da cigaba da kuma tabbatar da dorewar cigaban tattalin arziki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: