Gwamman fursunoni sun tsere daga gidan yarin Boma a yammacin Jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo

0 86

Gwamman fursunoni sun tsere daga gidan yarin Boma a yammacin Jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo.

Fursunonin sun yi amfani da sauti mai kara da aka kure yayin wata jana’iza a wani gida da ke makwaftaka da gidan yarin inda suka dauke hankalin masu gadin.

An dai kama fursunoni tara a cikin wadanda suka tseren a kusa da gidan yarin kuma an harbi daya daga cikin fursunonin bayan bindiga da masu gadin gidan yarin suka harba.

A halin yanzu akwai fursunoni 19 da ba a gansu ba. A baya dai an sha samun fursunoni na tserewa daga gidan yari a Boma.

Mazauna yankin da gidan yarin yake sun bayyana cewa gidan yarin na buƙatar gyara ganin cewa an gina shi ne tun a shekarun 1900.

Leave a Reply

%d bloggers like this: