Jam’iyyar APC a jihar Zamfara ta ce ta yiwa mambobi sama da miliyan 1 rajista a jihar

0 66

Jam’iyyar APC a jihar Zamfara a yau ta ce ta yiwa mambobi sama da miliyan 1 rajista a jihar.

Shugaban kwamitin rijistar ‘ya’yan jam’iyyar a jihar, Ibrahim Masari, ya bayyana hakan yayin gabatar da rahoton kwamitin ga gwamna Bello Muhammad Matawalle.

Mai magana da yawun gwamnan, Yusuf Idris, a cikin wata sanarwa, ya ce kwamitin ya bayar da rahoton cewa an yi wa mambobi miliyan 1 da dubu 20 da 800 rajista.

Ibrahim Masari ya nuna farin cikin sa ga dimbin ‘ya’yan jam’iyyar da suka fito domin yin rijistar, inda ya bayyana hakan a matsayin wanda ba a taba ganin irin sa ba kuma mai yawan jama’a.

Ibrahim Masari ya ce ba a samu wani cikas na tsaro ba yayin aikin rijistar.

Kamar yadda yazo cikin sanarwar, Ibrahim Masari ya kuma sake tabbatar da Gwamna Bello Muhammad Matawalle a matsayin uban jam’iyya wanda aka sani a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: